No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kamala Harris ta ƙira Trump domin taya murnar cin zaɓe

A jiya Laraba Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta ƙira Donald Trump domin taya shi murnar cin zaɓen shugaban ƙasa na bana, a cewar ɗaya daga cikin hadimanta, bayan zazzafar takarar da suka yi.

Harris ‘yar jam’iyyar Democrat ta tattauna da Trump a kan mahimmancin mika mulki cikin lumana da zama shugaban ƙasar dukkanin Amurkawa, a cewar hadimin dake bayani a madadinta.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna

Daga bisani Harris ta gabatar da jawabin amincewa da shan kaye a hannun abokin hamayyarta na jam’iyyar Republican kuma zaɓeɓɓan shugaban ƙasa Donald Trump.

Da safiyar jiya Laraba Trump ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka bayan da ya samu ƙuri’un wakilai 292 daga cikin 538.
A halin yanzu harris tana da ƙuri’un wakilai 224.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...