Ka yi adalci, ka muhimmantar da ‘yancin ɗan’adam – ‘Yan Shi’a ga Tinubu

0
350

Membobin ƙungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (almajiran Shaikh Zakzaky) wanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, sun yi ƙira ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta yi maganin tauye haƙƙn ɗan Adam da ake tafkawa a kan jagoransu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, da matarsa.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar a Abuja a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ƙungiyar ta bayyana wasu matsaloli na zalunci, da cin zarafi, da suka haɗa da kashe ‘ya’yan Shaikh Zakzaky da kisan kiyashi na Zariya, inda aka kashe sama da mutane 1,000. Wanda gwamnatocin baya ƙarƙashin jagorancin Goodluck Ebele Jonathan da Muhammadu Buhari suka yi.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci a sako ‘yan ƙungiyar da ake tsare da su na tsawon shekaru ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba.

KU KUMA KARANTA: Mabiya shi’a a Najeriya sun nemi kotu da ta dakatar da El-Rufai kan shirin rusa musu kadarori

‘Yan Shi’an sun buƙaci a saki Malam Haruna Abbas, Malam Ibrahim Hussaini, da Malam Adamu Suleiman ba tare da wani sharaɗi ba, waɗanda ake tsare da su tun a shekarar 2013, tare da gurfanar da waɗanda suka yi kisan gilla ga ‘ya’yan Shaikh Zakzaky guda uku da sauran membobi 31 a cikin shekarar 2014.

Da yake magana a madadin Almajiran Shaikh Zakzaky, Farfesa Shehu Maigandi, ya kuma buƙaci a gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda suka shirya kisan kiyashin Zariya kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada da kuma yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa da suka dace, da kuma a saki masu zanga-zangar Free Zakzaky, Ibrahim Khalid ba tare da wani sharaɗi ba, da wasu 49 da aka tsare tun ranar 22 ga Yuli, 2019.

‘Yan Shi’a sun ci gaba da neman a cire wa Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai ɗakinsa passport na tafiye-tafiye tare da fitar da takardun tafiyarsu ba tare da wani sharaɗi ba, wanda hukumar leƙen asiri ta ƙasa NIA da DSS suka ƙwace a lokacin da ake duba lafiyarsu a tafiyarsu zuwa Indiya.

Farfesa Maigandi ya bayyana cewa taron manema labarai na da nufin tunatarwa ga sabuwar gwamnati alhakin da ya rataya a wuyanta na magance take haƙƙin ɗan Adam a baya da kuma tabbatar da adalci ga waɗanda aka zalunta a jihar.

A cewarsa, “bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, don haka muna neman abubuwa kamar haka: a saki ‘yan uwa uku Malam Haruna Abbas, Malam Ibrahim Hussaini, da Malam Adamu Suleiman ba tare da wani sharaɗi ba, waɗanda ake tsare da su tun a shekarar 2013.

“A gurfanar da waɗanda suka aikata laifin kisan ‘ya’yan Shaikh Zakzaky uku da wasu talatin da daya (31) a ranar 25 ga Yuli, 2014; “A saki Malam Hassan Muhammad ba tare da wani sharaɗi ba da sauran ‘yan uwa da ake tsare da su a gidajen yari daban-daban ba bisa ƙa’ida ba, ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

“Bincike tare da gurfanar da wanda ya shirya kisan kiyashin Zariya da kuma hukunta shi bisa tanadin dokokin Najeriya da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da suka dace.

“Sakin masu muzaharar Free Zakzaky ba tare da wani sharaɗi ba, Ibrahim Khalid da wasu 49 da ake tsare da su tun ranar 22 ga Yuli, 2019.

“Cire dokar hana fita da aka yi wa Sheikh Ibraheem Zakzaky da matarsa, da kuma fitar da takardun tafiyarsu ba tare da wani sharaɗi ba.” inji Farfesa Maigandi

Leave a Reply