Kaɗaici na kashe sama da mutane 871 a duk shekara — WHO

0
617
Kaɗaici na kashe sama da mutane 871 a duk shekara — WHO

Kaɗaici na kashe sama da mutane 871 a duk shekara — WHO

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa akalla mutane 871,000 ke mutuwa a duniya a duk shekara saboda kadaici.

A cewar kwamitin WHO, daya cikin kowane mutane shida a fadin duniya na fama da kadaici — wanda tare da kebe kai daga al’umma — na iya janyo cututtuka na jiki.

Ta bayyana cewa kadaici na kara hadarin kamuwa da bugun zuciya, bugun jini (stroke), ciwon siga, damuwa (depression), fargaba (anxiety), da kuma kashe kai.

KU KUMA KARANTA:WHO ta koka kan yadda ƙwararru suka kasa gano dalilin ɓarkewar cutar Corona

WHO ta kara da cewa matasa masu kadaici na da yuwuwar samun sakamako mai rauni da kashi 22% fiye da abokan karatunsu, yayin da manya masu fama da kadaici ke fuskantar matsaloli wajen samun ko rike aikin yi.

Illar kadaici ba ta tsaya ga mutum daya ba kadai — illa ce da ke shafar al’umma gaba daya, tare da haddasa asarar biliyoyin kudade ga tsarin kiwon lafiya da kuma fannin aikin yi.

Shugaban kwamitin WHO, Vivek Murthy, ya bayyana kadaici da cewa: “Wani zafi ne da mutum ke ji daga cikin zuciyarsa idan dangantakar da yake bukata ba ta daidaita da irin wacce yake da ita.”

Leave a Reply