No menu items!

Sample Page Title

Date:

JUNE 12: “Ku kira ni da duk sunan da kuke so,” Inji Tinubu, Yana alƙawarin kare yancin faɗin albarkacin baki

Daga Jameel Lawan Yakasai 

Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya yi alkawarin kare haƙƙin dimokuraɗiyya na ‘yan Najeriya na ‘yancin faɗar albarkacin baki.

A cikin jawabin Ranar Dimokuraɗiyya da ya gabatar a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Shugaban ya ce wa jami’an tsaro kada su tsananta wa waɗanda ke sukar manufofin gwamnatinsa da ake ganin ba su yi wa jama’a daɗi ba.

“Dimokuraɗiyya na buƙatar haƙuri da kalamai masu zafi da cin mutunci,” a cewar Tinubu a gaban ‘yan majalisa daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

KU KUMA KARANTA: June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe

“Ku kira ni da duk sunan da kuke so, ku faɗi abin da kuke so, amma ni zan ci gaba da kira ga dimokuraɗiyya ta kare haƙƙinku na yin hakan.”

Tinubu ya shawarci magoya bayansa da ‘yan majalisa su fifita tattaunawa fiye da mulkin danniya, su fifita shawo kan juna fiye da tilastawa, da kuma kare haƙƙoƙin jama’a fiye da amfani da ƙarfi.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...