Jirgin yaƙin Nijar ya kashe fararen-hula bisa kuskure

0
119

Ma’aikatar Tsaro ta Jamhuriyar Nijar ta ce wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman ƙasar ya kashe fararen-hula bisa kuskure a harin da ya kai wa ‘yan ta’adda a jihar Tillaberi da ke kan iyaka da Burkina Faso.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da aka karanto a gidan talbijin na ƙasar RTN ranar Asabar da maraice.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami’an tsaro sun hango wani gungun ‘yan bindiga a kan babura yana tsara yadda zai kai hare-hare a yankin Libiri Bulangiga da Garbunwa ranar Juma’a da daddare zuwa Asabar da safe.

Daga nan ne aka bai wa jirgin yaƙi umarnin kai musu hari kuma an yi nasarar kashe ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ƙara da cewa washegari da jami’an tsaro suka je yankin da lamarin ya faru don duba halin da ake ciki sun gano cewa jirgin yaƙin ya kashe fararen-hula, ko da yake ba ta faɗi adadin waɗanda suka mutu ba.

Ma’aikatar Tsaron ta ce an kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawa.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta tabbatar mutum 85 sojoji suka kashe bisa kuskure a Kaduna

A wata sanarwa ta daban, Ma’aikatar Tsaron Nijar ta ce wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman kasar ya yi hatsari a kan iyaka da Burkina Faso.

Sanarwar ta ce jirgin ya faɗi ne ranar Juma’a da misalin ƙarfe 12:15 na rana.

“Jirgin rundunar sojojin saman Nijar ya yi hatsari ne a yayin da yake ƙoƙarin sauka a wani sansanin sojoji da ke garin Kantchare kusa da iyaka da ƙasar Burkina Faso,” in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ta ce babu wanda ya rasu ko da yake jirgin ya lalace sannan jami’i ɗaya da ke cikinsa ya samu rauni, wanda nan-take aka yi masa magani.

Leave a Reply