An daƙile wani bala’i a ranar Laraba yayin da wani jirgin sama mallakar ‘United Nigeria Airlines’ ya fice daga titin jirgi mai lamba 18 na hagu na filin jirgin Murtala Mohammed, a Legas.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, shugaban sashen sadarwa na kamfanin, Achilleus-Chud Uchegbu, ya ce ba a samu asarar rai ba.
Ya ce kamfanin jirgin ya sanar da hukumomin da abin ya shafa, kuma suna kokarin gano abubuwan da suka faru a cikin wannan matsala.
“Jirgin mai lamba 5N-BWW ɗauke da fasinjoji 50 yana tashi daga filin jirgin saman Abakaliki na jihar Ebonyi lokacin da lamarin ya faru.
“Jirgin ya sauka lafiya amma an tilasta masa ya dakatar da motsinsa zuwa gefen titin jirgin.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 14, ya jikkata 5 a Bauchi
Sanarwar ta ce dukkan fasinjojin sun sauka lafiya, kuma an ɗauke su zuwa zauren isowa tare da kayansu.
“Jami’an hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN, suna wurin da lamarin ya faru kuma tare da injiniyoyin UNA suna aikin kwashe jirgin.
“An kuma sanar da NCAA da AIB yadda ya kamata kuma suna wurin. United Nigeria tana ba da cikakken haɗin kai da hukumomi,” inji shi.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa kamfanin zai ci gaba da kiyaye tsauraran matakan tsaro a cikin ayyukansa tare da ba da fifiko ga lafiyar fasinjoji a kowane lokaci.