Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗi a jihar Neja

0
297

Mazauna ƙauyen Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja sun yi gudun hijira zuwa yankunan Erena da Zumba da Gwada a cikin Shiroro, biyo bayan wani hatsarin jirgin sama mai sauƙar ungulu na sojojin saman Najeriya (NAF) a yankinsu.

Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro, Aƙilu Ishaku ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna, ranar Litinin.

Ya ce ya samu labarin hatsarin jirgin ne daga jami’an tsaro da ke yankin da Hakimin Galkogo da sauran masu ruwa da tsaki a yankin da lamarin ya faru.

“A matsayina na babban jami’in tsaro na ƙaramar hukumar Shiroro, na samu rahoton hatsarin jirgin sama, amma rahoton bai bayyana takamaimai na jirgin ba.

KU KUMA KARANTA: Mutane huɗu sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

“Sunan ƙauyen da hatsarin ya auku shi ne ƙauyen Badna da ke ƙarƙashin gundumar Kwaki Chukuba.

“Mutanen sun yi iƙirarin cewa sun ga wuta daga nesa kuma sun ga wani jirgi mai sauƙar ungulu ne ke ci da wuta,” in ji shi.

Ishaku ya bayyana cewa lamarin ya sanya mutanen yankin tserewa da gudu domin tsira sakamakon fargaba inda suke samun mafaka a Erana, Zumba da Gwada.

NAN ta ruwaito cewa NAF a cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin jirginta ya yi hatsari a ƙauyen Chukuba da ke jihar Neja.

Ya ce jirgin ya taso ne a makarantar firamare ta Zungeru a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna, amma daga baya aka gano cewa ya yi hatsari a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Nijar.

Rundunar sojin sama ta ce jirgin na cikin aikin kwashe mutanen da hatsarin ya rutsa da su. Sanarwar ta ce “Jirgin Mi-171 mai sauƙar ungulu a aikin kwashe mutanen da suka jikkata ya yi hatsari da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ƙauyen Chukuba a Nijar.

Leave a Reply