No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jirgin ‘Max Air’ ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Jigin saman Max Air ƙirar Boeing 737 wanda ya dauko fasinjoji daga Jihar Lagos zuwa Jihar Kano ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano a daren jiya Talata.

Wasu da abun ya faru a akan idanun su sun ce dirar jirgin ke da wuya tayar gaba ta fashe, kuma ta kama da wuta. Daga nan sai jirgin ya yi taga-taga, goshinsa ya tunkuyi ƙasa.

KU KUMA KARANTA:Jirgin Max Air ya tsallake rijiya da baya sakamakon fashewar tayoyi a Yola

Tuni dai ma’aikatan kwana-kwana su ka daƙile faruwar gobara a jirgin, kuma fasinjoji su ka yi maza su ka fito daga jirgin.

Rahonanni sun nuna cewa babu asarar rayuka ko rauni ga fasinjoji da ma’aikatan jirgin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...