Jihar Yobe ta samu ci gaba ta fannoni da dama a ƙarƙashin Gwamna Buni – Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe, ta ce sun ga ci gaba ƙarƙashin gwamnatin Mai Mala Buni ta fuskar gina hanyoyin cikin gari da hanyoyi tsakanin garuruwa a faɗin jihar Yobe a ziyarar da ƙungiyar ‘yan jaridar ta yi a kwanakin baya.

Shugaban ƙungiyar ‘yan jaridar, Kwamared Rajab Mohammed Ismail ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan rangadin da ƙungiyar ta kai a baya-bayan nan domin gane wa kansu irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar da na ƙananan hukumomi ke yi na inganta rayuwar al’ummar jihar.

Rajab ya bayyana cewa, rangadin ya ba da damar ganewa kansu ƙoƙarin da majalisar jiha da ƙananan hukumomin jihar ke yi na inganta rayuwar al’umma ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ayyukan da aka gani a ƙasa yayin rangadin da ‘yan jarida suka yi sun haɗa da sauye-sauye a fannin ilmin addini, bunƙasar ababen more rayuwa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni suna da matuƙar farin ciki da cikar buƙatunsu.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya bada tallafin naira miliyan 100 ga waɗanda gobarar kasuwar Damaturu ta shafa

Shugaban ƙungiyar ta NUJ ya ci gaba da cewa, a fannin kiwon lafiya da ilimi, gwamna Mai Mala Buni ya kafa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 140 waɗanda suka kawo ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma musamman waɗanda suke tun asali.

Ya ci gaba da bayyana cewa, tsarin ilimi ma yana cika, domin a yanzu ɗalibai suna taƙama da saka sakamakon jarabawar WAEC, NECO da NABTEB a shafukan sada zumunta, gwamnati ta biya kuɗin jarabawa da kuma kuɗaɗen rajista na ƙwararru kamar na Nigerian Law School, ANAN da I CAN na wasu daga cikinsu.

“NUJ ta samu ta kuma kai ziyarar gani da ido a aikin gina kasuwar zamani a garuruwan Damaturu, Nguru da Gashuwa, waɗanda tuni an kammala su. Yayin da waɗanda ke Potiskum da Geidam ke dab da kammalawa.

“Muna matuƙar godiya ga gwamnan jihar Yobe bisa soyayyar da yake da ita ga kafafen yaɗa labarai a jihar, haƙiƙa shi ne gwamnan da ya fi kowa ƙulla-alaƙa da ‘yan jarida a Najeriya,” in ji shugaban ƙungiyar NUJ na Yobe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *