Janye tallafin Amurka zai shafi yaƙi da Polio a Afghanistan da Pakistan – WHO
A ranar Laraba ne, wani babban jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya yi jan hankali kan cewa, shafe cutar Polio a ƙasashen Afghanistan da Pakistan, kasashe 2 kacal da suka rage masu dauke da cutar da ta ki ci ta ki cinyewa, na fuskantar barazana sakamakon dakatar da samar da kudade daga Amurka.
A yayin wani taron manema labarai ta yanar kizo, daraktan yanki na gabashin Bahar Rum, Haan Balkhy, ya jaddada muhimmancin rawar da Amurka ke takawa a bangaren tallafin kudi ga kokarin kungiyar na sa ido kan cutar Polio da ma daukacin cututtuka masu yaduwa, musamman a wannan yankin.
KU KUMA KARANTA:Da ƙyar na sha a Yemen – Shugaban WHO
A makon jiya ne, shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin dakatar da kusan duk wani tallafi na waje, na tsawon kwanaki 90, domin ba gwamnatin sa damar tantance ko zai ci gaba da bayar da kudi ga dimbin ayyukan jinkai, da na ci gaban kasashe da shirye shiryen tsaro da ke samun taimako daga Amurka.
Haka zalika a ranar farko da Trump ya koma fadar white House ya sanar da ficewar Amurka daga hukumar lafiya ta duniya WHO.