Jam’iyyun APC da NNPP sun umurci magoya bayansu da su tare a cibiyoyin tattara zaɓe a Kano

3
347

Jam’iyyar APC da NNPP a jihar Kano sun ɓukaci magoya bayansu da su yi tattaki zuwa wuraren tattara sakamakon zaɓe.

Yayin da Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na NNPP, ya yi wannan kiran a madadin jam’iyyarsa, mai magana da yawun ƙungiyar yakin neman zaɓen Gawuna/Garo, Malam Muhammad Garba, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyya mai mulki da su tare a wajen tattara sakamakon zaɓen.

A wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Asabar, Garba ya ce ƙiran ya zama dole domin baiwa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar damar yin taka-tsan-tsan da zagon ƙasa ko sauya sakamakon zabe.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama wata mata ɗauke da kayan zaɓe na INEC a Legas

Hakazalika, Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya buƙaci ɗaukacin magoya bayan jam’iyyar da su mamaye cibiyoyin domin tabbatar da an kirga ƙuri’u.

A wani takaitaccen sakon bidiyo, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa daga sakamakon da aka tattara ya zuwa yanzu, jam’iyyarsa tana da yaƙinin lashe zaɓen gwamnan da za a yi ranar Asabar.

Ya ce dole ne a raka ƙuri’un daga rumfunan zaɓen zuwa wuraren tattara sakamakon.

“Ina godiya ga ɗaukacin magoya bayan Kwankwasiyya da NNPP bisa haɗin kan da suka ba su.

“Amma kuma ina kira ga ’yan kishin ƙasa da su tabbatar sun bi tsarin tsare ƙuri’un har zuwa cibiyoyinsu na RAC, da ƙananan hukumomi da ma matakin jiha.

“Muna da rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu makiyan jihar nan na ƙoƙarin yin amfani da wannan damar don kawo cikas ga lamarin,” in ji Kwankwaso.

3 COMMENTS

Leave a Reply