Jami’yyar adawa ta karɓe mulki a Birtaniya

0
87
Jami’yyar adawa ta karɓe mulki a Birtaniya

Jami’yyar adawa ta karɓe mulki a Birtaniya

Jami’yyar adawa ta Labour ta kawo ƙarshen shekara 14 na mulkin Jam’iyyar Conservative a ƙasar Birtaniya.

Kazalika Labour ta ƙwace kujerar tsohuwar fira ministar Birtaniya Liz Truss da ke wakiltar mazabar Norfolk ta Kudu maso Yamma a Majalisar Dokokin ƙasar.

Jam’iyyar Labour ta kafa tarihin doke Conservative ne bayan zaɓen ranar 5 ga watan Yuli inda ta samu rinjayen kujeru a majalisar dokokin ƙasar.

A yayin da zaɓen ke ci gaba da kirga ƙuri’u, Fira Minista Rishi Sunak, ya amsa shan kayi.

Ya sanar da cewa, “na ɗauki laifin wannan faɗuwa da muka yi.”

Da wannan shan kaye, Rishi Sunak zai sauka daga kujerar Fira Ministan, wadda Shugaban Jam’iyyar Labour, Keir Starmer, zai ɗare domin kafa sabuwar gwamnati.

KU KUMA KARANTA: Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Yobe — Jam’iyyun Adawa

Da yake jawabi, Starmer ya ce, “yau mun buɗe wani sabon babi a Birtaniya.”

Ya ci gaba da cewa, “nasarar zaɓe ba daga sama take faɗowa ba, sai da yaki da gwagwarmaya.

“Shi ya sa a wannan karo Jam’iyyar Labour ta kai ga narasa.”

Leave a Reply