Jam’iyar APC a Jigawa ta dakatar da wani shugaban jam’iyar a jihar, bisa zargin fyaɗe

Jam’iyyar ‘All Progressives Congress’ (APC) reshen jihar Jigawa, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Roni.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyar na jihar, Hon.Aminu Sani Gumel ya fitar.

An kama Saleh Idris mai shekaru 56 da laifin yiwa ‘yar aikin gidansa fyade.

A halin da ake ciki kuma, hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta tabbatar da kama Saleh Idris.

Kakakin hukumar NSCDC na reshen jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, biyo bayan ƙorafin da ɗan’uwan yarinyar ya kai cewa wanda ake zargin ya yi wa ‘yar uwarsa ‘yar shekara 14 fyaɗe tare da yi mata ciki. Yarinyar ‘yar aikin gidansa ce.

KU KUMA KARANTA: Ya bi malamar addini har cikin Coci ya yi mata fyaɗe

“Yadda lamarin ya faru shi ne lokacin da wanda ake zargin ya ba ta abin sha a lokacin da matarsa ba ta gida wanda hakan ya sa ta suma kuma ya yi mata fyaɗe.

“Lokacin da yarinyar ta farfaɗo, sai ya yi mata barazanar cewa ka da ta gaya wa kowa ko kuma ta yi kasadar rasa alawus ɗin ta na wata-wata, sakamakon haka, wannan mummunar ɗabi’a ta ci gaba da maimaituwa ba tare da ta faɗa wa kowa ba har lokacin da ciki ya bayyana.

CSC Adamu ya ce da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya musanta zargin kuma an kai ƙararsa zuwa kotu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *