Jami’o’i 18 da Najeriya ta haramta bayan rahoton kammala digiri a makonni 6

0
117

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da tantance takardun shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo biyo bayan rahoton jaridar Daily Nigerian da ya bankaɗo yadda ake samun Digiri a Makonni shida (6) a jamhuriyar Benin.

Ma’aikatar ilimi ta Najeriya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ma’aikatar ta lura cewa matakin da ta dauka ya biyo bayan wani binciken ɓoye da Jaridar Daily Nigeria ta gudanar wanda ya fallasa ayyukan sayar da digiri a Cotonou.

Kamar yadda binciken ya nuna, ɗan jaridar ya samu digiri a jami’ar Cotonou a cikin makonni shida, sannan kuma ya shiga cikin shirin da hukumar yi wa ƙasa hidima ta ƙasa NYSC ta shirya.

Ga jerin sunayen jami’o’in da hukumar kula da jami’o’in Najeriya ta haramta, kamar yadda ta wallafa a shafin yanar gizonta.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta soke tantance takardun digiri na jami’o’in Benin da Togo

  1. University of Applied Sciences and Management, Port Novo, Republic of Benin, ko wani reshen dake Najeriya.
  2. Volta University College, Ho, Volta Region, Ghana ko wani reshen dake Najeriya.
  3. The International University, Missouri, USA, Kano and Lagos Study Centers; ko wani reshen dake Najeriya.
  4. Collumbus University, UK da suke Najeriya
  5. Tiu International University, UK da suke Najeriya.
  6. Pebbles University, UK da suke Najeriya.
  7. London External Studies UK da suke Najeriya.
  8. Pilgrims University operates da suke Najeriya.
  9. West African Christian University da suke Najeriya.
  10. EC-Council University, USA, Ikeja Lagos Study Centre.
  11. Concept College/Universities (London) Ilorin ko wani reshen dake Najeriya.
  12. Houdegbe North American University campuses a Najeriya.
  13. Irish University
    Business School London, dake Najeriya.
  14. University of Education, Winneba, Ghana, dake Najeriya.
  15. Cape Coast University, Ghana, dake Najeriya.
  16. African University Cooperative Development, Cotonou, Benin Republic, dake Najeriya.
  17. Pacific Western University, Denver, Colorado, Owerri Study Centre.
  18. Evangel University of America da Chudick Management Academic, Lagos

Leave a Reply