Jami’in NSCDC ya haddasa hargitsi bayan ya bindige ɗalibai 2 a makarantar sakandare a Abuja

0
240

Aƙalla ɗalibai biyu na wata makarantar sakandare da ba a bayyana ba da ke unguwar Gwarinpa a Abuja, an yi zargin jami’an hukumar tsaro ta NSCDC ya harbe su har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba yayinda aka tura jami’an NSCDC da ke ofishin babban birnin tarayya Abuja domin samar da tsaro a yayin gudanar da jarrabawar.

Rikicin ya haifar da hargitsi a kusa da harabar makarantar amma jami’an ‘yan sanda da suka isa wurin sun cafke jami’an NSCDC tare da kwantar da hankula.

KU KUMA KARANTA: Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya bada umarnin kamo sufeton da ya harbi mutane uku a Kurna

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, “An samu wani lamari a wata makarantar sakandare. Nan take muka je wurin, kuma a halin yanzu, ina iya tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin”.

Adeh ta ce kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Garba Haruna ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin sanin yadda lamarin ya faru.

Leave a Reply