Jami’an zaɓe na Jamhuriyar Benin sun ziyarci INEC don ƙara inganta aiki

0
19
Jami’an zaɓe na Jamhuriyar Benin sun ziyarci INEC don ƙara inganta aiki

Jami’an zaɓe na Jamhuriyar Benin sun ziyarci INEC don ƙara inganta aiki

Wata tawaga mai mambobi 12 daga Hukumar Zaɓe Mai Cin Gashin Kanta ta Jamhuriyar Benin (CENA) ta ziyarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a wata ziyarar neman ƙarin sani.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Sacca Lafia, shugaban CENA, ta ƙunshi kwamishinonin ƙasa, direktoci, da manyan ma’aikata.

The Cable ta rawaito cewa an tarbi tawagar a ranar Litinin daga Mahmood Yakubu, shugaban INEC, tare da sauran mambobin hukumar a hedkwatar INEC da ke Abuja.

A cewar Lafia, manufar ziyarar ita ce domin koyon darussa daga tsarin zaɓen Najeriya da kyawawan ayyukanta, yayin da Jamhuriyar Benin ke shirin gudanar da zaɓen ta na 2026 mai zuwa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin haske kan ziyarar da shugaba Tinubu zai kai Qatar

Da yake jawabi a taron, Yakubu ya jaddada muhimmancin wannan ziyara da kuma ƙalubalen da CENA ke fuskanta kafin zaɓen.

“Farkon watan da ya gabata, mun karɓi wasiƙa daga CENA da ke nuna sha’awar su ta yin wata ziyarar karatu zuwa INEC Najeriya yayin da suke shirin gudanar da abin da suka kira mafi rikitarwa daga cikin zabukan su a shekarar 2026,” in ji shi.

Leave a Reply