Gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaron ƙasar za su haɗa gwiwar domin soma yin dirar mikiya kan mutanen da ke sanya dala ta yi tsada.
Wannan aiki zai kasance na haɗin gwiwa tsakanin Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ONSA, da kuma Babban Bankin Ƙasar CBN, a ƙoƙarinsu na magance matsalolin da ke kawo tarnaƙi ga yanayin tattalin arzikin ƙasar, a cewar wata sanarwa da ofishin na ONSA ya fitar a ranar Talata.
Matakin na zuwa ne a lokacin da farashin dala ke sake yi tashin gwauron zabi a kasuwannin musayar kuɗaɗe, inda naira take ci gaba da durƙushewa, inda a yanzu dala ɗaya take a madadin sama da naira 1,800.
Hukumomin biyu sun ce maƙasudin wannan aikin haɗin gwiwa shi ne don a dinga gano masu ɓoye dalar, da gudanar da bincike a kansu da kumayi musu hukuncin da ya dace, walau a ɗaiɗaiku ko a ƙungiyance.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Katsina ya saka hannu kan dokar haramta ɓoye abinci
Sanarwar ta ce “Matakan yunƙurin da CBN ya ɗauka na daidaita kasuwar musayar kuɗaɗe da zaburar da harkokin tattalin arziki abin yabawa ne.
“To amma ayyukan wasu mutane a ciki da wajen ƙasar na daƙushe tasirin waɗannan tsare-tsare ta hanyoyi daban-daban, wanda hakan ke ƙara ta’azzara faɗuwar darajar nairar da kuma haifar da hauhawar farashin kayayyaki da taɓarɓarewar tattalin arziki.”
Da yake lissafo irin matakan da CBN ya ɗauka don magance matsalar, Ofishin ONSA a sanarwar ya ce an samar da dabarun haɓaka ƙimar naira a cikin kasuwannin musayar kuɗaɗe, da mayar da farashin dala a CBN daidai da a kasuwannin bayan fage, da biyan bashin da ake bin ƙasar na daloli da kuma gabatar da sabbin hanyoyin aiki ga ma’aikatan kasuwannin musayar kuɗi.
Kazalika, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta samar da wata tawaga ta musamman ta mutum 7,000 a shiyyoyinta 14, domin daƙile masu ɓoye dala.
Sai dai duk da waɗannan matakai da ake ɗauka, hukumomin sun ce bayanan sirri sun nuna yadda ake ci gaba da daƙile darajar nairar a kasuwannin musayar kuɗaɗe na Najeriya.
“Shi ya sa Ofishin ONSA da CBN suka haɗa gwiwa a kan wannan muhimmin matakin don magance matsalar. Wannan haɗin gwiwa za ta haɗa da wasu muhimman hukumomi, ciki har da Rundunar Ƴan sanda da EFCC da Hukumar Kwastam da kuma Hukumar Leƙen Asiri kan hada-hadar kuɗaɗe, (NFIU).
Hukumomin biyu sun bayyana fatan cewa wannan matakin zai inganta tsarin gwamnati na yaƙi da masu halatta kuɗin haram tare da kawo daidato a bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.