No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga shida tare da ƙwato makamai a jihohin Kaduna da Katsina.

A jihar Katsina ’yan sanda sun hallaka ’yan bindiga uku suka kuma ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a yankin Gogalo da ke ƙaramar hukumar Jibia.

Maharan sun shigo ƙauyen ne ɗauke da muggan makamai, inda suka sace mutum uku.

Daga bisani ’yan sanda suka bi sawu, suka hallaka uku daga cikinsu sannan suka ƙwato waɗanda aka sacen.

KU KUMA KARANTA: Za mu inganta tsaro ta hanyar haɗa kan jami’an tsaro da tattara bayanan sirri

A jihar Kaduna, sojojin sun hallaka ’yan bindigar ne a yankin ƙananan hukumomin Kajuru da Birnin Gwari na jihar.

Sun kuma kama bindigogi ƙirar AK47 da sauran makamai da wayoyi, wasu kuma suka tsere da raunukan harbi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...