No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an tsaro sun damƙe wani ɗalibi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi ɗauke da bindiga da harsashi.

Ɗalibin ɗan aji 3 uku ne, kuma ’yan sanda sun cafke shi ne da bindigar  hannu ce bayan ya fito daga harabar jami’ar da ita,

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Wakil ya ce ana kama ɗalibin ne a lokacin da yake ƙoƙarin haɗa wasu gungun ɗalibai.

Wakil ya ce ɗalibin ya gaya musu cewa hayar bindigar ya karɓo na shekarar karatu guda daga wurin wani.

KU KUMA KARANTA: An kama ’yan sanda suna gadin dillalin miyagun ƙwayoyi

Ɗalibin ya shaida musu cewa ya karɓo bindigar ce domin kare kansa daga masu aikata muggan laifuka.

Jami’in ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Mohammed Musa, ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin ɗalibin na mallakar bindigar da kuma ko ya taɓa amfani da ita sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...