Jami’an tsaro su ɗauki duk matakin da ya dace kan masu ɓoye kayan abinci – Tinubu

0
172

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwar kafa rundunar ‘yansandan jihohi a ƙasar.

Wannan dai na daga cikin batutuwan da aka tattauna a wajen wani taron gaggawa da ya yi da gwamnonin jihohin ƙasar 36 ranar Alhamis a fadarsa.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan nazarin muhimman matsalolin da ke addabar ƙasar yanzu da zimman nemo bakin zaren warware su.

Batutuwan dai sun haɗa da na tsaro, da tsadar rayuwan da ƙarancin abinci da makamantansu kamar yadda ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya sanar da manema labarai bayan tashi daga zaman.

Ya ce zaman ya ƙunshi shawarwari kan yadda za a haɗa kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.

”Ba ma son rabe-rabe tsakanin jihohi da gwmnatin tarayya, ko da a wace jam’iyya kake, an yi shawawara kan yadda za a ciyar da ƙasar gaba”, in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta rufe rumbunan masu ɓoye abinci 5

Dangane da ‘yan sandan jihohi, ministan ya ce shugaba Tinubu ya amince cewa a duba maganar yiwuwar kafa ‘yansandan ciki a faɗin jihohin ƙasar, maimakon dogara da ‘yan sandan gwamnatin tarayya.

”To sai dai wani abu ne da yake buƙatar nutsuwa a duba a kuma tantance, ba abu ba ne da kawai za a faɗa cikinsa kai tsaye, yana buƙatar nazari sosai”, in ji ministan yaɗa labaran.

Ministan ya ƙara da cewa taron ya amince da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar su yi aiki tare da gwamnonin jihohi wajen sa ƙafar wando ɗaya da waɗanda suka ɓoye kayan abinci da muhimman kayan masarufi domin su yi tsada sannan su sayar da su.

Haka kuma shugaban ƙasar da gwamnonin sun kuma amince cewa ƙasar ba ta buƙatar shigo da kayan abinci daga waje, domin sauƙo da farashinsa, suna masu cewa ƙasar na iya dogara da abincin da al’ummarta ke nomawa.

Wannan taron dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP suka yi wani taron inda suka kwatanta halin da ƙasar ta shiga ta fuskar taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tashin farashin kaya da rashin tsaro da irin wanda ƙasar Venezuela ta shiga a shekarun baya.

Ko a jiya ma dai majalisar sarakunan gargajiya ta ƙasar ta yi wani taro a Kaduna inda ta nuna damuwa game da ƙaruwar matsalolin tsaro da talauci da kuma rashin aikin yi tsakanin al’ummar ƙasar musamman a yankin na arewa.

Leave a Reply