Jami’an tsaro a Neja sun gano bama-bamai da aka binne

0
81
Jami’an tsaro a Neja sun gano bama-bamai da aka binne

Jami’an tsaro a Neja sun gano bama-bamai da aka binne

Jami’an tsaro a Jihar Neja, sun gano wasu bama-bamai da abubuwan fashewa da yawa a wurare daban-daban da aka binne a wasu yankunan jihar.

Wuraren da aka binne bama-baman sun haɗa da yankin Galadima-Kogo a Ƙaramar Hukumar Shiroro, yankin Mutun-Daya a ƙaramar hukumar Munya, da yankin Gbeganu da ke Minna.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Katsina sun kama matashin da ya sare hannun ƙanin mahaifinsa

Ya bayyana cewa an gano abubuwan fashewar ne yayin ayyukan yaki da ta’addanci tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.

A Galadima-Kogo, wani bam ya tashi a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC).

An ɓoye abubuwan fashewar ne a wurare daban-daban, amma tawagar ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro a jihar sun gano su, inji kakakin ‘yan sandan.

Abiodun, ya ƙara da cewa an lalata bama-baman a ranar 22 ga watan Agusta, 2024, a bayan Dutsen Zuma da ke Suleja.

Ya ce aikin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin SP Mohammed Mamun, wanda ke kula da sashen lalata bama-bamai na rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here