Jami’an NSCDC 3,542 ne za su kula da wuraren bukukuwan kirsimeti da murnar sabuwar shekara a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rundunar tsaro da ke bayar da kariya ga al’umma da muhimman kadarori (Civil Defence) ta kasa reshen jahar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan ta, Mohammed Lawal Falala, ya bayar da umarnin tura jami’an hukumar 3,542 don kula da sha’anin tsaro a wuaren da Ake bukukuwan Kirsimeti a fadin jahar.
Kakakin hukumar reshen jahar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai ,
KU KUMA KARANTA:Ƙananan yara da yawa sun mutu a turmutsitsi a wajen bikin ƙarshen shekara
Sanarwar ta ce dakarun , za su kula da Chochi da kuma sauran wuraren da al’umma za suje don gudanar da bukukuwan sabuwar shekara da kuma na Kirsimeti.
Haka zalika, hukumar tsaron civil defence, din ta kara da cewa za su Yi aikin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, musamman wadanda suke bayar da gudunmawa wajen kula da Ababen hawa da Zirga-Zirgarsu don tabbatar da an Yi komai lafiya.
SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya ce Kwamandan Rundunar, ya kuma bayar da umarnin kama duk Wanda ya Yi Yunkurin tayar da fitina ko yin kafar ungulun da zai kawo rashin zaman lafiya don ya fuskanci hukunci.
A karshe hukumar ta ce za su ci gaba da Sanya Ido a muhimman wuraren, don tabbatar da kare kadarorin Gwamnati da na al’umma.