Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto wasu mutane bakwai da suka maƙale a ƙarƙashin wata katanga da ta ruguje a dandalin Malam Ƙato da ke kusa da Shagon Sufaye a cikin birnin Kano.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Lahadi a Kano.
Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar.
“Mun samu ƙiran waya daga wani Malam Bashir Mansur da misalin ƙarfe 05:43 na rana cewa bango ya rushe.
KU KUMA KARANTA: Ɗaliba ta tayar da gobara a makaranta saboda an ƙwace mata waya, 19 sun mutu
“Bayan samun labarin, mun yi gaggawar aika ‘yan kwana-kwana zuwa wurin da abin ya faru da misalin ƙarfe 05:47 na yamma,” in ji shi.
Ya ce wani gefen katangar da ke dandalin Malam Ƙato ya ruguje ya kuma shafi mutane bakwai.
Ya bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa da Abubakar Abdullahi mai shekaru 30; Abdulsalam Idris, 20, Usman Abdullahi, 20, Usaini Muhammed, 30, Umar Isah, 40.
Abdullahi ya ce, ‘yan kwana-kwana sun ceto dukkan waɗanda abin ya shafa da ransu, inda ya ce biyar daga cikinsu da ƙananan raunuka an kai su asibitin koyarwa na Abdullahi Wasai yayin da wasu biyu da suka samu munanan raunuka aka garzaya da su asibitin Albarka domin kula da lafiyarsu.
Ya ce ba a rasa rai ba, inda ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
[…] KU KUMA KARANTA: Jami’an kashe gobara sun ceto mutum 7 daga katangar da ta ruguje a Kano […]