Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga ECOWAS

0
135

Daga Ibraheem El-Tafseer

Uku daga cikin ƙasashen da sojoji suke jagoranta a yammacin Afirka sun ce za su fice daga ƙungiyar raya tattalin azriƙin yankin ta ECOWAS saboda takunkumin da aka ƙaƙaba musu.

Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da haka ne ta cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, suna cewa ECOWAS ta gaza taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.

“Bayan shekaru 49, gwarazan al’umar ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun yi takaicin yadda ECOWAS ta sauƙa daga kan turbar da aka kafa ta, kamar yadda Kanar Amadou Abdramane, shugaban da ke jagorantar sojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya karanta.

KU KUMA KARANTA: Firaiministan Nijar, Lamine Zeine, ya caccaki ECOWAS  kan yin zagon ƙasa

ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumai tare da dakatar da su daga ƙungiyar, biyo bayan ƙwace iko da sojoji suka yi a jerin juyin mulkin da suka yi, abin da ya haifar da fargaba ta ɓangaren siyasa a Sahel.

Leave a Reply