Jagororin muslumi a Benuwe sun yi taron gaggawa kan kisan gillar musulmi a jihar

0
137
Jagororin muslumi a Benuwe sun yi taron gaggawa kan kisan gillar musulmi a jihar

Jagororin muslumi a Benuwe sun yi taron gaggawa kan kisan gillar musulmi a jihar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jagororin al’umma Musulmi a jihar Benue sun gudanar da wani taron gaggawa domin tattaunawa bayan kisan gillar da wasu ɓata gari suka yi wa wasu matasa biyu ’yan asalin jihar Kano a unguwar Agan da ke Makurdi.

Taron ya tattauna kan yadda za a kawo karshen ayyukan taʼaddanci a tsakanin alʼumma da kuma buƙatar Musulmai na a tabbatar da tsaro da adalci ga waɗanda aka kashe.

KU KUMA KARANTA: Rundunar Ƴansanda ta Kano ta gano AK-47 ta bogi a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan DPO na Rano

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugaban Jamaʼatu Nasril Islam na jihar Benue, Alhaji Garba Baba (AGB), mataimakin limamin Makurdi, Sheikh Idris Musa Imam, da Sarkin Hausawan Makurdi, Alhaji Baba Yusuf Mai Kyau sai mai ba gwamnan Benue shawara kan harkokin Musulunci Hon. Umar Hassan Abdullahi.

An kuma yi addu’ar Allah ya jikan matasan da aka kashe da rahama, tare da fatan hukumomi za su ɗauki matakin da ya dace kan lamarin.

Leave a Reply