Iyaye mata sun yi zanga-zanga a Kano, saboda yawaitar faɗan daba 

0
334
Iyaye mata sun yi zanga-zanga a Kano, saboda yawaitar faɗan daba 
Mata suna zanga-zanga a Kano

Iyaye mata sun yi zanga-zanga a Kano, saboda yawaitar faɗan daba

Daga Jameel Lawan Yakasai

Iyaye mata da yan mata ne suka fito zanga-zangar suna kira a kawo karshen fadan daban dake haddasa asarar rayukan yayansu babu gaira babu dalili.

Yanzu haka dai tuni jami’an tsaro suka isa wajan domin kwantar da tarzoma.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da alummar unguwar ke alhinin rasa rayukan wasu da ake zargin yan daba da kashewa sakamokon fadan dabar da ya barke a jiya Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Faɗan daba a Kano, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da ɓarnata da dukiyoyi

Masana da dama na dora alhakin wanzuwar fadan daba tsakanin matasa sakamokon rashin aikin yi da kuma karancin ilimi.

Wannan lamari na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin Kano ta gabatar da sabbin jami’an da zasu dakile masu sana’ar kwacen waya da kuma fadan daba.

Leave a Reply