Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce Tel Aviv a shirye take ta “zafafa” hare-haren da take kaiwa Gaza idan aka gaza cimma nasarar amincewa da sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a yankin Falasɗinu, a tattaunawar sulhu da ake yi a Masar.
Gallant ya ce Isra’ila ta shirya tsaf domin ganin ta kuɓutar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, in ji Gallant bayan da ya zagaya yankin Rafah biyo bayan kutsen da Isra’ila ta yi a kan iyakar Rafah da ke kudancin yankin.
Amma “idan aka cire wannan batun a tattaunawar, to mu ci gaba da zafafa hare-haren,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
KU KUMA KARANTA: Tankokin yaƙin Isra’ila sun shiga kudancin birnin Rafah na Gaza — Rahoto
Kalaman Gallant na zuwa ne bayan da masu shiga tsakani na Isra’ila suka isa birnin Alkahira domin yin wani yunƙuri na baya-bayan nan na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ta kwashe watanni bakwai tana yi a Gaza.