Isra’ila za ta sallami wasu sojojinta na shirin ko-ta-kwana daga yaƙin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila za ta sallami wasu daga cikin sojojinta na shirin ko-ta-kwana da ke yaki a Gaza, a wani mataki da ta ce zai taimaka wa tattalin arzikinta a yayin da ƙasar take shirin ƙaddamar da dogon yaƙi a yankin.

“Wasu daga sojojin shirin ko-ta-kwana za su koma wurin iyalansu da kuma bakin aikinsu a wannan makon,” a cewar kakakin rundunar sojin Isra’ila Rear Admiral Daniel Hagari.

“Hakan zai bunƙasa tattalin arziki, sannan ya ba su damar samun kuzari a jikinsu gabanin ayyukan da za su yi a wannan shekarar, kuma za mu ci gaba da yaƙi, kana za mu buƙace su.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *