Isra’ila tana aikata kisan kiyashi ba tare da wata shakka ba – Jami’in MƊD

0
126

Mutum sama da miliyan ɗaya da suka yi gudun hijira daga Gaza zuwa birnin Rafah da ke kudancin yankin, na cikin fama da matsanancin ƙaranci abinci da ruwa da tsaftar muhalli, da sauran buƙatu na yau da kullum, kamar yadda wani wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman ya shaida wa Anadolu.

“Sama da mutum miliyan ɗaya ne suke cunkushe a Rafah, waɗanda suka yi gudun hijira daga wasu sassan Gaza, kuma suna fama da ƙarancin kayan masarufi na yau da kullum, daga abinci da ruwa da tsaftar muhalli tare da barazanar cututtuka fiye da duk wani abu da muka gani na wani rikici a cikin ‘yan shekarun nan a duniya,” in ji Balakrishnan Rajagopal, wakilin MƊD na musamman kan ‘yancin samun gidaje.

KU KUMA KARANTA: Ƙasashen Larabawa sun nemi MƊD ta dakatar da Isra’ila daga mamaye Rafah

Ya ƙara da cewa “Ba a taɓa samun wani yanayi da ba za ma a bar jama’a ko guduwa su yi ba.”

Yayin da yake jaddada yadda masu aiko da rahotanni na MƊD suka rubuta rahotanni da dama kan “kisan kare dangi” na hare-haren Isra’ila a Gaza, Rajagopal ya bayyana cewa, sun ambaci “mummunan haɗarin kisan kiyashi” a cikin rahotonsu na farko.

Leave a Reply