Isra’ila ta ƙaddamar da wani hari a tsakiyar Beirut

0
39
Isra'ila ta ƙaddamar da wani hari a tsakiyar Beirut

Isra’ila ta ƙaddamar da wani hari a tsakiyar Beirut

Dakarun Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da sanyin safiyar Litinin a yankin Kola na birnin Beirut, wanda ya kasance irinsa na farko da suka kai a cikin babban birnin na Lebanon tun da suka soma yaƙi da Hezbollah a watan Oktoban da ya wuce.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa jirgi mara matuƙi na Isra’ila ya kai hari a hawa na biyar na wani gida a kan hanyar da ta haɗa Beirut da Filin Jirin Saman Ƙasa da Ƙasa na Rafik Hariri.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu bari Isra’ila ta kori Falasɗinawa ba – Sarkin Jordan 

Harin ya tayar da gobara a gidan, ko da yake ‘yan kwana-kwana sun kashe ta.

Daga bisani ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) ta tabbatar da cewa harin ya kashe shugabanninta uku: Mohammed Abdel Aal, wani mamba na ɓangaren siyasarta kuma shugaban sashen soja da tsaro; Imad Ouda, kwamanda soji na Lebanon, da Abdel Rahman Abdel Aal, wanda ba a bayyana matsayinsa ba.

Leave a Reply