No menu items!

Sample Page Title

Date:

Isra’ila ta kutsa kai cikin sansanonin Falasɗinawa, inda rikici ya ɓarke

Sojojin Isra’ila sun kai farmaki a garin Tulkarem da sansanin ‘yan gudun hijira na Balata da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Dakarun mamaya na Isra’ila sun mamaye Tulkarem bayan tsakar dare, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa Wafa ya bayyana.

Rahoton ya ƙara da cewa, wasu motocin sojojin mamaya tare da rakiyar manyan buldoza guda biyu sun shiga birnin daga ɓangarensa na yammacin ƙasar, inda suka fara rusa ababen more rayuwa a yankin Al-Alemi, yayin da wani jirgin sama mara matuƙi na sa ido ya yi ta shawagi ta saman birnin.

Wafa ya kuma ruwaito cewa, sojojin Isra’ila sun kai farmaki sansanin ‘yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus tare da rakiyar buldoza ta soji, lamarin da ya kai ga arangama da dakarun gwagwarmayar Falasɗinawa.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Shaidun gani da ido sun ce an yi arangama tsakanin Falasɗinawa da sojoji a kofar shiga sansanin.

Masu fafutuka sun yaɗa bidiyon da ke nuna motocin soji da kuma buldoza yayin farmakin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...