Isra’ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza da raunata 310

0
108

Aƙalla Falasɗinawa 174 Isra’ila ta ƙara kashewa sannan ta raunata 310 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.

“Ƴan Isra’ila masu kama wuri zauna sun yi kisan kiyashi kan iyalai 18 a Zirin Gaza, inda mutum 174 suka rasu tare da raunata 310 a sa’o’i 24 da suka gabata,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa.

KU KUMA KARANTA: Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dole Isra’ila ta kaucewa kisan kiyashi a Gaza

“Akwai mutane da dama da har yanzu sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai da kan tituna yayin da masu aikin ceto suka gaza kaiwa gare su,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here