Isra’ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

0
102

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 28, cikinsu har da ƙananan yara da dama, a sabbin hare-hare da ta kai wurare daban-daban a yankin Gaza da ta mamaye, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World da kafafen watsa labaran yankin.

Jiragen yaƙin Isra’ila sun kashe mutum takwas a yankin Tuffah bayan sun kai hari kan wata motar ƴan sanda. Kazalika luguden wutar da Isra’ila ta yi a sansanin al-Maghazi da ke yankin Deir al-Balah na Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 13.

Haka kuma Isra’ila ta kashe Falasɗinawa bakwai a harin da ta kai wa wasu iyalai a sansanin Yabna da ke birnin Rafah. Ta jikkata mutane da dama a harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here