Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

0
144

Jami’ai sun ce sojojin Isra’ila sun kashe wani ɗan jarida a Gaza, abin da ke nufin kawo yanzu sun kashe ‘yan jarida 106 tun da suka ƙaddamar da hare-hare a yankin.

An kashe ɗan jaridar da ke aiki da gidan talbijin na Al Quds TV tare da wasu iyalansa a hari ta sama da sojojin Isra’ila suka kai gidansu a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, a cewar jami’an lafiya da abokansa ‘yan jarida.

Ƙungiyar da ke kare hakkin ‘yan jarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ) a makon jiya ta ce makonni 10 na farkon yakin da Isra’ila ke yi a Gaza su ne mafi muni da ‘yan jarida suka fuskanta, inda wannan shekarar ta kasance wacce aka fi kashe ‘yan jarida a wuri ɗaya.

Galibin ‘yan jaridar da Isra’ila ta kashe Falasɗinawa ne. Rahoton ƙungiyar CPJ da ke da cibiya a Amurka ya ce ta yi “matuƙar damuwa musamman kan yadda sojojin Isra’ila suke kai hari kan ‘yan jarida da iyalansu da gangan.”

KU KUMA KARANTA: Hamas ta ce kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza yana da muhimmanci

A farkon watan nan, wani binciken kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gano cewa wata tankar yaƙin Isra’ila ce ta kashe ɗan jaridar Reuters, Issam Abdallah, da kuma jikkata ‘yan jarida shida a Lebanon ranar 13 ga watan Oktoba ta hanyar yin luguden wuta a kansu a yayin da suke ɗaukar labarai kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a kan iyaka.

Leave a Reply