Isra’ila ta kashe mutum 78 a hare-haren da ta kai Gaza a jajiberin Kirsimeti

0
147

Jami’an lafiya na Falasɗinu sun ce wasu hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai a jajiberin Kirsimeti sun yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 78.

Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren ne da tsakar daren Litinin inda ta wayi garin yau tana luguden wuta musamman a yankin Al Bureij da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda ganau da kafafen watsa labarai na Falasɗinu suka tabbatar.

An kashe aƙalla mutum 70 a hari ta sama da jiragen yakin Isra’ila suka kai yankin Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar Falasɗinu Ashraf Al Qidra, yana mai cewa galibinsu mata ne da ƙananan yara.

KU KUMA KARANTA: An kashe sojojin Isra’ila takwas a Gaza, an yi wa shida mummunan rauni

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana nazari kan abin da ya faru a Maghazi kuma tana so ta rage yawan fararen-hular da ke cutuwa. Ƙungiyar Hamas ta musanta zargin da Isra’ila ke yi mata cewa tana buya a wuraren da ke da dandazon jama’a inda take yin amfani da mutanen a matsayin garkuwa.

Ƙungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta wallafa bidiyoyin mutanen da suka jiakkata a yayin da ake tafiya da su asibiti. Ta ce jiragen yaƙin Isra’ila sun yi ta luguden wuta a manyan hanyoyin da ke tsakiyar Gaza, inda suka hana motocin ɗaukar marasa lafiya wucewa.

Leave a Reply