No menu items!

Sample Page Title

Date:

Aƙalla Falasɗinawa 15 Isra’ila ta kashe a harin da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, da kuma sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasɗinawa ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce jiragen yakin Isra’la sun kai harin ne da asubahi a gidaje biyu da ke Khan Younis.

Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa an kashe farar hula 13 a lokacin da jirgin ya kai hari kan gidan iyalan Zuhd da ke sansanin Nuseirat sannan wata mace da danta suka rasu a wani hari da jirgin sojin ya kai a gidan iyalan Abu Akar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...