Isra’ila ta kashe manyan jami’an sojin Iran a harin da ta kai ta sama

0
96

Manyan sojojin Iran aƙall 13 ne suka mutu, ciki har da zaratan soji bakwai na runduna ta musamman ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), a harin da aka ɗora wa Isra’ila alhakin kai shi.

Cikin waɗanda aka kashe har da Janar Mohammad Reza Zahedi, babban kwamanda na Dakarun Quds da ke rundunar IRGC a Syria da Lebanon, da mataimakinsa Janar Hadi Haj Rahemi.

A yayin da Isra’ila ta kwashe fiye da wata shida tana kai hare-hare a Gaza, Katz ya ƙi faɗin takamaimai ranar da dakarun sojinsu za su shiga Rafah da ke kudancin yankin.

“Na san cewa Isra’ila za ta shiga Rafah, amma ba na so na yi ƙarin bayani,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Ana tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Isra’ila da Iran yayin da suke barazanar kai wa juna hari

Duk da Allah wadarai da ƙasashen duniya suke yi da Isra’ila kan mawuyacin halin da ta jefa Falasɗinawan da ke Gaza a ciki, tuni firaiministan Isra’ila ya sha alwashin kai hari a Rafah da ke kudancin yankin inda Falasɗinawa kusan miliyan biyu suke samun mafaka.

Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba bayan Hamas ta kai mata harin ba-zata, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 1,200.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu, dakarun Isra’ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 33,300 tare da jikkata sama da mutum 76,000 da kuma lalata galibin gine-ginen da ke Gaza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here