No menu items!

Sample Page Title

Date:

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 7 tare da raunata wasu da dama

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla bakwai tare da raunata wasu da dama a hare-haren da ta kai ta sama a Gaza da ta yi wa ƙawanya.

Sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata rumfa da ke gefen titi da ake sayar da kayayyaki a yankin Qizan Abu Rashwan da ke kudancin Khan Younis, inda suka kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

A wani harin da Isra’ila ta sake kai wa, wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu cewa Falasɗinawa uku ne suka mutu, wasu goma kuma suka jikkata, yawancinsu kananan yara, a wani harin da aka kai ta sama a wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu bari Isra’ila ta kori Falasɗinawa ba – Sarkin Jordan 

A cewar majiyar, daya daga cikin waɗanda suka jikkata ya rasu kafin a isa Asibitin Al-Awda da ke Nuseirat, yayin da wasu goma suka samu raunuka.

An kai wasu “sassan jikin” mutum biyu da abin ya shafa asibitin shahidan Al-Aqsa, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...