Isra’ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

0
49
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare ta sama da samame da ta kai a wasu garuruwa da ke arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent.

KU KUMA KARANTA: An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

Jiragen yaƙin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas, in ji Ahmed Jibril, jami’in ƙungiyar bayar da agajin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here