Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ta’azzara

0
154

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na WAFA ya rawaito cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa uku a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye.

An kashe mutanen ne a harin da aka kai a garin Tubas da kuma sansanin Al-Far’a da ke kusa da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, in ji sanarwar.

Aƙalla Falasɗinawa 400 ne sojojin Isra’ila da wasu Yahudawa ƴan kaka-gida suka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Leave a Reply