Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 29 a harin da ta kai ta sama a wata makaranta da ‘yan gudun hijira suke samun mafaka a kudancin Gaza ranar Talata, a yayin da luguden wutar da dakatunta suke ci gaba yi a arewaci ya sa aka rufe asibitocin Birnin Gaza tare da tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu domin neman mafaka.
Sojojin Isra’ila sun yi kisan kiyashi a makarantar Al-Awda da ke garin Abasan na gabashin Khan Younis, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar.
Galibin yankunan Birnin Gaza sun kasance tamkar kufayi sakamakon luguden wutar da dakarun Isra’ila suka kwashe watanni tara suna yi a yankin. Yawancin mutanen da ke birnin sun tsere tun da aka fara yaƙin, amma dubban mutane na ci gaba da zama a arewaci.
KU KUMA KARANTA: An yi zanga-zangar neman ƙasashen Musulmai su tura sojoji don taimaka wa Falasɗinawa a Gaza
A watanni tara da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, dakarunta sun mamaye asibitoci aƙalla takwas, inda suka kashe majinyata da ma’aikatan kiwon lafiya tare da lalata gine-gine da kayan aiki.
Isra’ila ta yi zargin cewa ƙungiyar Hamas tana mafani da asibitocin ne domin ajiye makamai, ko da yake ba ta bayar da cikakkun shaidu game da zargin nata ba.
Asibitoci 13 daga cikin 36 da ke Gaza ne suke aiki a halin yanzu, kuma su ɗin ba ba sa aiki kamar yadda ya kamata, a cewar ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya.