No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Falasɗinu ta zargi sojojin Isra’ila da kashe Falasɗinawa 30 a Gaza.

“An gano gawarwakin mutum 30 da aka ɗaure wa hannu da kuma rufe musu idanu a cikin wata makaranta a Beit Lahia da ke arewacin Gaza,” in ji ƙungiyar fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Ya ce Falasɗinawan da suka mutu sojojin Isra’ila ne suka tsare su kafin mutuwarsu.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya za ta ci gaba da fallasa farfagandar Isra’ila – Altun

“A bayyane yake cewa sojojin mamaya sun aiwatar da hukuncin kisa a kan waɗannan mutane,” in ji ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ce hukumomin Isra’ila sun ƙi bayar da bayanai game da makomar Falasɗinawa da sojojin Isra’ila ke riƙe da su a Gaza.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...