Jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a ginin ƙungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent Society (PRCS) inda suka kashe mutum guda tare da jikkata mutum shida.
Ƙungiyar ta wallafa bidiyo da ya nuna cewa harin ya sauka a gininta da ke birnin Khan Younis.
Ƙungiyar ta PRCS, wadda ke bayar da agajin magunguna da na jinkai, ta fuskanci hare-hare a yakin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila za ta sallami wasu sojojinta na shirin ko-ta-kwana daga yaƙin Gaza
Kazalika Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 14, ciki har da ƙananan yara tara, a jerin hare-haren da ta kai a yammacin birnin Khan Younis na Gaza, a cewar ma’aikatar kiwon lafiya ta yankin.