Isra’ila ta bai wa kashi 20 na Falasɗinawan da ke Khan Younis wa’adi

0
89

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra’ila ta fitar da wani sabon wa’adi, inda ta umarci mazauna yankunan babban birnin Gaza da aka yi wa ƙawanya da su gudu.

Ofishin kula da ayyukan jinƙai na MƊD, OCHA, ya ce Isra’ila ta fitar da taswirori da ke nuna sabbin wuraren da suka shafi kusan kashi 20 cikin 100 na birnin Khan Younis da aka yi wa ‘yan gudun hijira.

Kafin faɗan ya ɓarke, yankin na da mutane sama da 110,000, in ji OCHA.

Ya kuma ƙara da cewa yankin ya haɗa da matsuguni 32 da ke ɗauke da ‘yan gudun hijira sama da 140,000, waɗanda akasarin su a baya sun yi gudun hijira daga arewa.

Leave a Reply