Isra’ila ta ɗauki matakin daƙile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar Falasɗinu ta MƊD a Birnin Kudus da ta mamaye

Isra’ila ta ƙaddamar da matakan dakatar da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) daga ayyukanta a Gabashin Birnin Kudus, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Isra’ila suka bayyana.

Shafin watsa labarai na Times of Israel ya rawaito cewa, ministan gidaje na Isra’ila Yitzhak Goldknopf a ranar Litinin ya rubuta wasika zuwa ga daraktan hukumar kula da filaye ta Isra’ila kan korar UNRWA daga duk wani abin da ake kira wata kasa a Birnin Kudus.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah

Ya ba da umarnin “dakatar da” duk wata yarjejeniya tsakanin hukumar da hukumar kula da filaye.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *