Isra’ila na tsoro kada Amurka ta amince da ƙasar Falasɗinu

0
124

Isra’ila na cike da tsoro game da matakin Amurka na neman a kafa ƙasar Falasɗinu a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da yankin Gaza da aka mamaye, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka rawaito.

“Majiyoyi na siyasa sun bayyana damuwarsu game da matakan da gwamnatin Amurka take ɗauka cikin gaggawa na samar da ƙasar Falasɗinu a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza da aka mamaye a ƙarƙashin sabon tsari na Hukumar Falasɗinu,” a cewar jaridar Maariv ranar Juma’a.

“A cewar jami’an gwamnatin Amurka, Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje tana duba yiwuwar amincewa da ƙasar Falasɗinu a wani babban tsari na siyasa,” in ji jaridar.

Jaridar ta bayyana cewa idan hakan ya faru za a samu “juyin-juya-hali na siyasa.”

Kawo wannan lokaci, duka gwamnatocin da suka gabata a Amurka sun ƙi amincewa da ƙasar Falasɗinu, suna masu hakan zai faru ne idan Falasɗinawa da Isra’ilawa suka amince da yarjejeniyar kafa ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Iraƙi ta haramta wa wasu bankunan ƙasar 8 hada-hada da Dalar Amurka

Washington ta ƙalubalanci zaman Falasɗinu cikakkiyar ƙasa a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya inda ta riƙa hawa kujerar-na-ƙi a Kwamitin Tsaro na Majalisar, na baya bayan na shi ne wanda ta yi a 2011.

Amma Isra’ila ta soma lura da himmar da gwamnatin Biden take yi ta amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu ko da kuwa ba tare da yardarta ba, in ji jaridar.

“Kwanakin baya Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bai wa ma’aikatan ofishinsa umarni su tsara takardu na yiwuwar Amurka ta amince a kafa ƙasar Falasɗinu ba tare da neman yardar Isra’ila ba,” kamar yadda jaridar ta rawaito.

Leave a Reply