Iska mai ƙarfi tarushe garuruwa da dama a Kano

0
163
Iska mai ƙarfi tarushe garuruwa da dama a Kano

Iska mai ƙarfi tarushe garuruwa da dama a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Iska mai karfi ta rushe gidaje da dama a garuruwan Dogara, Sitti da Dambazau a Sumaila da ke Kano.

Lamarin ya farune a daren Laraba, wadda Jihar Kano ta samu iska mai karfin gaske a cikin dare, da kuma ruwa, sai dai ruwan bai sauka da yawa ba.

KU KUMA KARANTA: Gini ya rufto akan ɗalibai a GGSTC Potiskum, ɗaliba 1 ta rasu, 5 suna kwance a Asibiti

Wasu Mazauna garuruwan da abun ya shafa sun bayyanawa Jaridar Neptune Prime cewar lamarin ya faru ne cikin daren Laraba wayewar garin Alhamis da misalin karfe 2 na dare,

Inda suka ce iskar ce ta fara tashi sosai sai daga baya kuma ruwa ya sauka, haka kuma sunyi kira ga Gwamnati da ta kawo musu dauki, sakamakon asarar da ta same su na iftila’i.

Leave a Reply