Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama
Daga Ibraheem El-Tafseer
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasar Ebrahim Raisi ya rasu bayan wani hatsarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi.
Wani jami’in gwamnatin ƙasar ta Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewa shugaban ƙasar ya rasu ne tare da ministan harkokin waje Hossein Amirabdollahian.
Har ila yau daga cikin waɗanda suka rasu a hatsarin, akwai Gwamnan Gabashin Lardin Azerbaijan, Malek Rahmati da Limamin Tabriz, Imam Mohammad Ali Alehashem da shugaban jami’an tsaron tawagar da babban dogara shugaban ƙasar da shugaban ma’aikatan jirgin da kuma matuƙa jirgin su biyu.
KU KUMA KARANTA: Jirgi mai sauƙar ungulu ɗauke da shugaban ƙasar Iran Ra’isi, ya faɗi
Ana sa ran a rantsar da mataimakin shugaban ƙasar ta Iran na farko, Mohammad Mokhber a matsayin sabon shugaban ƙasa.
Masu hasashe dai na bayyana fargabar mutuwar Shugaba Raisi na iya sake jagula rikicin gabas ta tsakiya wanda Isra’ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa tun bayan ƙaddamar da hare-haren a yankin Gaza, saboda nuna ɗan yatsa da za a yi ga Isra’ila da aminiyarta Amurka saboda yadda sa-in-sa ta ɓarke a tsakanin Iran da Isra’ila bayan harin da Isra’ila ta kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran a Siriya da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran.
Ita ma Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare da jirage marasa matuƙa kimanin 300 inda suka lalata wasu wurare na sojoji a Isra’ila yayin da kuma Ingila da Amurka suka yi iƙirarin sun tare galibin jirage da makaman da Iran ta harba a kan Isra’ila.