Connect with us

Ƙasashen Waje

Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Published

on

Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban ƙasar, Ebrahim Ra’isi, a hatsarin jirgin sama

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasar Ebrahim Raisi ya rasu bayan wani hatsarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi.

Wani jami’in gwamnatin ƙasar ta Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewa shugaban ƙasar ya rasu ne tare da ministan harkokin waje Hossein Amirabdollahian.

Har ila yau daga cikin waɗanda suka rasu a hatsarin, akwai Gwamnan Gabashin Lardin Azerbaijan, Malek Rahmati da Limamin Tabriz, Imam Mohammad Ali Alehashem da shugaban jami’an tsaron tawagar da babban dogara shugaban ƙasar da shugaban ma’aikatan jirgin da kuma matuƙa jirgin su biyu.

KU KUMA KARANTA: Jirgi mai sauƙar ungulu ɗauke da shugaban ƙasar Iran Ra’isi, ya faɗi

Ana sa ran a rantsar da mataimakin shugaban ƙasar ta Iran na farko, Mohammad Mokhber a matsayin sabon shugaban ƙasa.

Masu hasashe dai na bayyana fargabar mutuwar Shugaba Raisi na iya sake jagula rikicin gabas ta tsakiya wanda Isra’ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa tun bayan ƙaddamar da hare-haren a yankin Gaza, saboda nuna ɗan yatsa da za a yi ga Isra’ila da aminiyarta Amurka saboda yadda sa-in-sa ta ɓarke a tsakanin Iran da Isra’ila bayan harin da Isra’ila ta kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran a Siriya da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran.

Ita ma Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare da jirage marasa matuƙa kimanin 300 inda suka lalata wasu wurare na sojoji a Isra’ila yayin da kuma Ingila da Amurka suka yi iƙirarin sun tare galibin jirage da makaman da Iran ta harba a kan Isra’ila.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra’ila kan Shugaba Erdogan

Published

on

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra'ila kan Shugaba Erdogan

Turkiyya ta yi tur da kalaman ministan Isra’ila kan Shugaba Erdogan

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi Allah wadai da wani saƙo da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Israel Katz ya wallafa a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan kan shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na Isra’ila na ɓoye laifukanta.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a ranar Talata ta ce “Muna daukar wannan matsayi na rashin mutuntawa da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila ke yi wa mai girma shugaban kasarmu a matsayin wani lamari da za a ji shi ne kawai daga bakin ƙasar da ake zarginta da kisan kiyashi.”

Yayin da take suka da kakkausar murya a shafukan sada zumunta, ma’aikatar ta ce: “Irin wannan ƙazafi da ƙarya wani ɓangare ne na ƙoƙarin Isra’ila na ɓoye laifukan da ta aikata.”

Turkiyya ta ƙara da cewa, za ta ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da adalci.

KU KUMA KARANTA: Ana lalata mutuncin bil’adama a Gaza – Ministan Turkiyya

Isra’ila, wadda ta yi fatali da ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman tsagaita wuta cikin gaggawa, ta fuskanci tofin Allah-tsine a tsakanin kasashen duniya a ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Fiye da Falasɗinawa 37,700 aka kashe tun daga lokacin a Gaza, yawancinsu mata da yara, kuma kusan wasu 86,400 sun jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Sama da watanni takwas da yakin Isra’ila a Gaza, inda yankuna da dama suka zama kufai a cikin yankin da aka yi wa ƙawanya da hana shigar da abinci da ruwan sha da magunguna.

Ana tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Duniya, wanda hukuncin na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasɗinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Shugaba Ruto na Kenya ‘ba zai’ sa hannu a kan sabuwar dokar ƙarin haraji ba

Published

on

Shugaba Ruto na Kenya 'ba zai' sa hannu a kan sabuwar dokar ƙarin haraji ba

Shugaba Ruto na Kenya ‘ba zai’ sa hannu a kan sabuwar dokar ƙarin haraji ba

Shugaban Kenya, William Ruto ya ce ba zai rattaba hannu kan wata doka mai cike da cece-kuce da ta haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar ba, har aka harbe mutane da dama.

Masu zanga-zangar sun mamaye majalisar ne bayan da ‘yan majalisar suka zartar da dokar a ranar Talata. Kudirin zai kara yawan haraji da kuma tsadar rayuwa.

“Bayan yin la’akari da ci gaba da tattaunawa game da abubuwan da ke ƙunshe a cikin kudirin kudi na 2024, da kuma sauraron jama’ar Kenya, wadanda suka yi kira da babbar murya cewa ba sa son wani abu da wannan ƙudirin kuɗi na 2024, na yarda, don haka ba zan sanya hannu ka dokar ba, kuma daga baya za a janye shi,” Ruto ya shaida wa taron manema labarai a fadar gwamnati da ke Nairobi babban birnin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru

“Mutane sun rasa rayukansu kuma abin takaici ne matuka, da ma hakan bai faru ba,” ya ƙara da cewa.

Zanga-zangar ta jawo gwamnati ta girke sojoji don shawo kan karya doka da oda.
Sai dai wata Babbar Kotu ta soke umarnin girke sojojin.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru

Published

on

Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru

Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru

Ƙungiyar likitoci ta Kenya ta ce adadin waɗanda suka mutu, sanadiyar zanga-zangar ƙarin kuɗin haraji da gwamnatin ƙasar ta sanar, ya ƙaru zuwa 13.

Shugaban Ƙungiyar Simon Kigondu ne ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP adadin, a wata zantawa da suka yi da shi a yau Laraba.

Masu zanga-zangar waɗanda yawancinsu matasa ne, sun mamaye zauren majalisar dokokin kasar a jiya Talata, inda suka rinka jifar ‘yan sanda da duwatsu da kuma rushe shingen jami’an tsaro don kutsa kai cikin harabar majalisar.

Bayan faruwar lamarin, shugaban ƙasar William Ruto ya tura da jami’an soji don tarwatsa masu zanga-zangar.

KU KUMA KARANTA: Mutum 12 sun mutu a rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Chadi

Shugaba Ruto ya lashi takobin ɗaukar tsauraran matakai don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar, inda ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.

Sai dai duk da ɗaukar wancan mataki, masu zanga-zangar sun ce babu gudu babu ja da baya game da ƙudirinsu na ci gaba da zanga-zangar, har sai haƙarsu ta cimma ruwa.

Wani jami’i a asibitin Kenyatta da ke birnin Nairobi, ya ce a asibitin kadai, jami’insu sun duba mutane 160 da suka samu raunukan harhasai wasu kuma kananan raunuka.

Ɗaya daga cikin abubuwan da masu zanga-zangar ke buƙata shi ne shugaban ƙasar William Ruto ya sauka daga muƙaminsa.

Matasan sun bayyana matakin gwamnatin Ruto na lafta wa jama’a haraji a matsayin wani sabon yunƙuri na jefa al’umma cikin ƙarin musiba, ganin yadda tuni matsalar tsadar rayuwa ta yi musu dabaibayi.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like