Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa

0
274

Iran ta gargaɗi Isra’ila da cewa za ta iya kai harin riga-kafi cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa’  idan har Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hamas a Gaza.

Tun bayan da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin ba-zata kan Isra’ila a ranar 8 ga watan Oktoba, inda ta kashe fararen hula fiye da dubu ɗaya tare da yin garkuwa da ɗaruruwan ‘yan Isra’ila, Isra’ila ta mayar da martani, inda ta kai hare-hare kan maɓoyar Hamas da ke Gaza tare da daƙile mai, abinci da ruwa, a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin mamaye Gaza.

Iran a ranar Talata, 17 ga Oktoba ta yi gargaɗin cewa wakilan ƙasar da ke yammacin Asiya za su iya kai hare-hare kan Isra’ila “a cikin sa’o’i masu zuwa”.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ganawar da ya yi da babban sakataren ƙungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a baya-bayan nan, ministan harkokin wajen ƙasar Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa: A cikin sa’o’i masu zuwa, duk wani mataki na turjiya kan gwamnatin sahyoniyawa abu ne mai yiwuwa.

KU KUMA KARANTA: Yaƙin Falasɗinawa da Isra’ila: An fara kwaso ’yan Najeriya da suke can

Shugabannin gwagwarmaya ba za su ƙyale gwamnatin sahyoniyawan ta yi duk abin da ta ga dama a Gaza ba, sannan ta koma wasu fagagen gwagwarmayar,” in ji Amirabdollahian.

Ministan na Iran ya ƙara da cewa ƙasarsa ba ta ba da umarni ba ga ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya a duk faɗin yankin amma tana goyon bayansu.

Amirabdollahian ya kuma yi barazanar idan yaƙin ya faɗaɗa zuwa wasu fagagen, “zai canza taswirar Isra’ila.

Leave a Reply